Saturday, 12 March 2022

HUKUNCIN JANABA ZAAD MUSLIMAT

*AL-MAR'A ASWALIHA HADITH CLASS*

*🌳BABIN HUKUNCIN JANABA🌳*
DARASI NA HUDU (4)

Hadith 1.

*"عن خولة بنت حكيم رضي الله عنها، أنها سألت النبي صلى الله عليه وسلم عن المرأة ترى في منامها ما يرى الرجل، فقال ليس عليها غسل حتى تنزل"*
رواه أحمد

*An karbo Hadith daga Khaulatu (RA), ta tambayi Manzon Allah (saw) game da macen da ta gani (ta yi mafarki) a cikin barcinta, irin yadda namiji yake gani (taga kamar ta sadu da namiji) sai ya ce mata, babu wanka a kanta har sai in tayi Inzali (in ta fitar da maniyyi)*

Hadith 2

*عن عائشة رضي الله عنها، أن رجلا سأل رسول الله صلى الله عليه وسلم، عن الرجل يجامع أهله ثم يكسل -وعائشة جالسة-فقال رسول الله صلى عليه وسلم، إني لأفعل ذلك أنا و هذه ثم نغتسل*

رواه مسلم

*An karbo Hadith daga Nana Aishatu (RA) , lallai wani mutum ya tambayi Manzon Allah (saw) ,game da mutumin da yake saduwa da iyalinsa, sannan kuma sai yaji yayi kasala- (lokacin) Nana Aishatu tana Zaune (a wajen) sai Manzon Allah (saw) ya ce masa, Nima hakan yana faruwa dani da wan nan(wato Aishatu) sannan kuma sai muyi wanka"*

Wan nan ke gwada ashe in har mutum ya fitar da Maniyy ko a barci ne ko ya tuna mai ya faru ko bai tuna ba, zai yi wankan Janaba, in kuma yayi mafarkin yayi abu da mace amma ya tashi baiga komai ba, ba wanka akansa kenan, hakan kuma ita ma macen abun yake kanta.

Sai kuma matsala ta gaba, idan mutum ya sadu da iyalinsa matukar al'auran sun shiga juna to dole ayi wanka, koda kuwa baa samu biyan bukatar duka ba, dan kasala ko wani abu ya saka aka rabu.

Allah ya kara banu fahimtar addininmu yadda ya kamata.
*________________________________*

No comments:

Post a Comment