Friday, 18 March 2022

FALALAN LOKACIN LA'ASAR

*⌛ AL-MAR'A ASSALIHA(MACE TA GARI)⌛*

*FALALAN LOKACIN LA'ASAR DIN RANAR JUMA'AH*
*⬛ فضلُ عصرِ يومِ الجمعة ⬛*

✍️ *Haruna Isah Muh'd*
*hdindima@gmail.com*

An samu Hadisi daga abu Huraira (RA), daga Manzon Allah (saw) ya ce :
*"A ranar Juma'ah akwai wata lokaci, ba musulmin da zai yi dace da ita, a samu kuma yana Addu'a a lokacin, ya kuma roki Allah wani Alkhairi (ko wani iri ne) , Face sai Allah ya bashi"*

▫️ عن أبي هريرة رضي الله عنه، عن رسول الله ﷺ أنه قال: *(إِنَّ فِي الْجُمُعَةِ لَسَاعَةً، لَا يُوَافِقُهَا مُسْلِمٌ، قَائِمٌ يُصَلِّي، يَسْأَلُ اللهَ خَيْرًا، إِلَّا أَعْطَاهُ إِيَّاهُ)،* وأشار بيده يُقلِّلها.
📜رواه البُخارِيُّ ومُسلِم

Ibn alQayyim (R) ya ce:
*" Wan nan lokaci kuwa ita ce karshen lokaci na Sallahr La'asar bayan ana idar da La'asar, Magabata na Kwarai suna girmama wan nan lokaci sosai"*

▪️ قال ابن القيم رحمه الله : 
*"وهذه الساعة هي آخر ساعة بعد العصر، تُعَظِّمُها جميع أهل الملل".*
📜زاد المعاد ١/٣٨٤

Bayani ya zo akan cewa, Daawus Ibn Kaisani (R) ya kasance idan ya yi Sallar La'asar na ranar Juma'ah, yakan zauna a wurin yana kallon Gabas, baya magana da kowa (yana Addu'a) har rana ta fadi
▪️ ورد أن طاووس بن كيسان رحمه الله كان إذا صلى العصر يوم الجمعة استقبل القبلة ولم يكلم أحدًا  حتى تغرب الشمس .

*"Haka kuma an samu a tarihi cewa Saeed Ibn Jubair (R) in yayi Sallahr La'asar na ran Juma'ah baya magana da kowa har rana ta fadi (yana Addu'a da salatin Manzon Allah (saw))"* yana tsoron kar wan nan lokaci mai tsada ta tafi bai ribaceta ba, kuma baya son ya rasa wan nan lokaci na amsa addu'o'in bayi.
 
*▪️ وكذلك ورد عن سعيد بن جبير رحمه الله أنه إذا صلى العصر من يوم الجمعة لم يكلم أحدًا حتى تغرب الشمس؛* خوفًا على هذا الوقت الفاضل من الضياع، وأن يحرم التوفيق لساعة الأجابة .

Ya kai Dan'uwana kai ma kayi kwadayin samun wan nan lokaci mai tsada mana, ta yadda zaka dinga rokon Allah duk wani damuwanka da alkhairi a wajensa na Duniya da lahira, ba mai dacewa sai wanda Allah ya datar dashi. Muna rokon Allah ya sa mu dace. Ameeeeen.

•• فاحرص على اغتنام هذه اللحظات العظيمة، وسَلْ الله تعالى من خيري الدنيا والآخرة، والموفق من وفقه الله، نسأل الله من فضله .

Fatan Alkhairi gareku  maza da mata baki daya.
 
Kaima ka tura don mu rabauta baki daya , kuma muyi tarayya cikin wan nan lada.
*_______________________________*

No comments:

Post a Comment