*AL-MAR'A ASSALIHA (ZAUREN MACE TA GARI)*
*NASIHA GA MA'AURATA*
*.. نصيحة للمتزوجين ..*
✍️ *Haruna Isah Muh'd*
*hdindima@gmail.com*
*ليس هناك زوج أو زوجة كاملين ..*
1. *_Ba miji ko macen da ya zama ya kammala (tara muke duka bamu cika goma ba)_*
*ولا خاليان من العيوب ..*
2. *_Ba wani miji ko matan da suka kubuta daga aibi, (duk kammu muna da namu laifin)._*
*أنت تكملها، وهي تكملك ..*
3. *_Kai mai gida, kai ka mayard da ita ta zama cikakkiyar mace, ita ma ita ce ta mayar dakai cikakken namiji_*
*أنت سترٌ لها، وهي سترٌ لك ..*
4. *_Kai ne fa kake mata sutura, ita ma tana maka sutura.(duk marar mata ana masa kallon garwa ne, ita kuma marar miji ana mata kallon baho ce)_*
*أنت تحتويها، وهي تحتويك ..*
5. *_Kai ne fa kake janta a jiki kake bata kulawa, ita ma hakan ne, ita ce take janka a jiki kuma take baka kulawa._*
*(هُنَّ لِبَاسٌ لَّكُمْ وَأَنتُمْ لِبَاسٌ لَّهُنَّ)*
*_(Su mata fa su ne suturanmu, muma sutura ne nasu)_*
*_Duk cikan mutum bai taba zama mutum sai yana da aure, ita ma mace hakan ne._*
*_Ashe ya kamata kowa yana hakuri da juna, kana gwada mata soyayya ita ma haka, dan kar ka taba jin wai kai ne ka mata alfarma, ita ma ta maka alfarma wlh._*
*_Mata muna girmama mazajenmu , suma suna girmamamu, sai kuga an zauna, zama mai kyau kuma mai dadi._*
*_Ka zame wa matarka tamkar Abu zar'in a wajen Ummu Zar'in, kema ki zama masa tamkar Ummu Zar'in a wajen Abu Zar'in._*
*______________________________*
No comments:
Post a Comment