AL-MAR'A ASWALIHA (ZAUREN MACE TA GARI)
YADA ALFAHASHA YANA DAGA CIKIN MANYA-MANYAN ZUNUBAI
⬛ إشاعة الفاحشة من كبائر الذنوب ⬛
▫️قال الله تعالى: *(إِنَّ الَّذِينَ يُحِبُّونَ أَنْ تَشِيعَ الْفَاحِشَةُ فِي الَّذِينَ آمَنُوا لَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ وَاللَّهُ يَعْلَمُ وَأَنْتُمْ لَا تَعْلَمُونَ)* 📜النور: 19
ALLAH (swt) ya ce:
*"Wadan da suke son yada alfahasha a tsakanin masu imani, suna da azaba mai radadi a nan Duniya da kuma Lahira, Allah shi ne masani ku baku sani ba"*
*▪️قال شيخ الإسلام ابن تيمية رحمه الله :*
قد توعّد بالعذاب على مُجرد محبّة أن تشيع الفاحشة بالعذاب الأليم في الدنيا والآخرة وهذه المَحبّة قد لا يقترن بها قولٌ ولا فعلٌ، فكيف إذا اقترن بها قولٌ أو فعلٌ؟ 📜مجموع الفتاوى
Shehul Islam Ibn Taimiyya yana cewa:
*"Ku duba fa, Allah yayi alkawarin zai yi azaba wa mutum don ya ji yana *son* *ya yada alfahasha, hakan fa mutum bai fa yada ba, yaji yana so ne, amma an ce zai tarar da azaba mai radadi tun anan duniya balle in an je lahira,*
*To ina kuma ga wanda ya ji yana son kuma ya yada?!*
▫️قال الله تعالى: *(لِيَحْمِلُوا أَوْزَارَهُمْ كَامِلَةً يَوْمَ الْقِيَامَةِ وَمِنْ أَوْزَارِ الَّذِينَ يُضِلُّونَهُمْ بِغَيْرِ عِلْمٍ أَلَا سَاءَ مَا يَزِرُونَ)* 📜النحل: 25
Allah (swt) ya ce:
*"Za su dauki nauyin zunubansu da kuma zunuban wadan da suka batar ba tare da ilimi ba, wan nan daukan nauyin laifi ya yi muni"*
▫️وفي الحديث : *(مَن سَن سُنّة سيئة فعليه وزْرُها ووزر مَن عمل بها إلى يوم القيامة)* 📜رواه مسلم
Manzon Allah (saw) ya ce:
*"Duk wanda ya fara kafa wata barna marar kyau, yana da zunubinsa da kuma na wadanda ya batar dasu (muddin suna aikatawa) har zuwa tashin al-Qiyama"*
Gaskiya anan muke jan hankalinmu baki daya da mu iya kokarinmu muga muna yada Alkhairi kuma mu guji yada (alfahasha) wa mutane da kuma duk wani abu na barna, dan ba zai tsaya a kansu su kadai ba, har damu wadan da muka fara yadawa.
Duk abun da kika san zaki tura ko zan tura mu tabbata ba zai bata tarbiyan al-Ummah ba.
Ayoyi da Hadith da suka gabata sun ishemu ishara, dan mu shiga taitayinmu.
A karshe ina mai mana fatan Alkhairi, Allah kuma ya hadamu baki daya a cikin gidan Aljannah, wadan da suka yi tunani da kuma assasa wan nan Zaure mai Albarka, *المرأة الصالحة* ALLAH ya sa ya zama dalilin shigansu Aljannah baki daya damu sauran mabiya. Ameeeeen
✍️ Haruna Isah Muh'd
hdindima@gmail.com
*_____________________________*
No comments:
Post a Comment