Thursday, 24 March 2022

FALALAN SAURARO DA ZAMA A WAJEN KARATUN ADDINI

*📚 AL-MAR'A ASSALIHA (ZAUREN MACE TA GARI) 📚*

*💥FALALAN SAURARO DA ZAMA A WAJEN KARATUN ADDINI💥*

_*🌱 فضل الجلوس لاستماع العلم*_

✍️ *Haruna Isah Muh'd*
*hdindima@gmail.com*

An samo Hadith daga abi Waqidil Laithy (RA) ya ce lallai Manzon Allah (saw) wata-rana yana zaune tare da mutane a masallaci, sai ga wasu mutane guda uku, biyu daga ciki suka fuskanci Manzon Allah (saw) sai daya daga cikinsu  ya koma.

⭕ عَنْ أَبِي وَاقِدٍ اللَّيْثِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ ، أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بَيْنَمَا هُوَ جَالِسٌ فِي الْمَسْجِدِ وَالنَّاسُ مَعَهُ، إِذْ أَقْبَلَ نَفَرٌ ثَلَاثَةٌ، فَأَقْبَلَ اثْنَانِ إِلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَذَهَبَ وَاحِدٌ، 

Sai ya ce : biyu daga ciki suka tsaya a wajen Manzon (saw) (don su saurari ilimin addini). Daya sai yaga wuri a cikin mutanen da suka kewaye Manzon Allah (saw), sai ya kutsa ya shiga ya zauna, shi kuma dayan sai ya zauna a bayansa ( sabo da kunyar kar ya shiga ya takura wa mutane), shi kuma dayan tun tuni ya juya ya tafi abinsa, da Manzon Allah (saw) ya gama ba da darasi sai ya ce:

قَالَ : فَوَقَفَا عَلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَأَمَّا أَحَدُهُمَا فَرَأَى فُرْجَةً فِي الْحَلْقَةِ فَجَلَسَ فِيهَا، وَأَمَّا الْآخَرُ فَجَلَسَ خَلْفَهُمْ، وَأَمَّا الثَّالِثُ فَأَدْبَرَ ذَاهِبًا، فَلَمَّا فَرَغَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ 

*"Shin kuna son in baku labarin wasu mutane guda uku? Daya daga cikinsu ya kusanci Allah sai kuma Allah ya jawoshi a jikinsa, shi kuma dayan yaji kunyar Allah, sai Allah ma yaji kunyansa, Amma shi kuma dayan ya bijire wa Allah, shima Allah ya bijire masa."*

*▪️قَالَ : أَلَا أُخْبِرُكُمْ عَنِ النَّفَرِ الثَّلَاثَةِ ؟ أَمَّا أَحَدُهُمْ فَأَوَى إِلَى اللَّهِ فَآوَاهُ اللَّهُ، وَأَمَّا الْآخَرُ فَاسْتَحْيَا فَاسْتَحْيَا اللَّهُ مِنْهُ، وَأَمَّا الْآخَرُ فَأَعْرَضَ فَأَعْرَضَ اللَّهُ عَنْهُ▪️*

📚 متفق عليه (66-2176)
*ــــــــــــ*

*NB*
_Lallai yan'uwana maza da mata sauraro da kuma tashi tsaye a nemi ilmin addinin Musulunci abu ne na dole, za muga yadda Manzon Allah (saw) ya yaba wa mutanen nan guda biyu, Ammaa shi daya fa, yadda ya guje ma sauraron ilmin addini shima hakan ne ya jawo masa Allah yayi baram-baram dashi._

*📜شرح الحديث📜*

*💡أنَّ النَّبيَّ صلَّى الله عليه وسلَّم كان جالسًا مع أصحابِه في المسجد، فأقبَل ثلاثةُ نفَرٍ، أي:* ثلاثة رجالٍ؛ أمَّا أحدُهم فولَّى وأعرَض ولم يأتِ إلى الحلقةِ، وأمَّا الثَّاني فوجَد في الحلقة فُرجةً فجلَس، وأمَّا الثَّالثُ فجلَس خلف الحلقةِ، كأنَّه استحيَا أن يُزحِمَ النَّاس وأن يضيِّقَ عليهم، فلمَّا فرغ النَّبيُّ صلَّى الله عليه وسلَّم قال: ألَا أُخبِركم بنبأ القومِ، أمَّا أحدهم فأوى إلى اللهِ فآواه اللهُ عزَّ وجلَّ، وهو الَّذي جلَس، فآواه اللهُ عزَّ وجلَّ إليه؛ لأنَّه كان صادقَ النِّية في الجلوس مع النَّبيِّ صلَّى الله عليه وسلَّم، فيسَّر اللهُ له، وأمَّا الثَّاني فاستحيَا فاستحيا اللهُ منه؛ لأنَّه ما زاحَم ولا تقدَّم، وأمَّا الثالثُ فأعرَض فأعرَض اللهُ عنه، لم يوفِّقْه لأنْ يجلسَ مع هؤلاء القومِ البَرَرةِ الأطهار.

Allah ka taimakemu baki daya, ka bamu ikon tashi tsaye don neman ilmin addinin Musulunci. Ameeeeen.

Tura ma yan'uwa dan muyi tarayya a cikin ladan baki daya.
*_____________________________*

No comments:

Post a Comment