Wednesday, 9 March 2022

DALILAN SAMUN KARIYAN ALLAH DAGA KO WANI IRIN SHARRI

*🌹AL-MAR'A ASWALIHA (MACE TA GARI)🌹*

*DALILAN SAMUN KARIYA DAGA ALLAH*

*⬛ من أعظم أَسباب الحفظ ⬛*

*Sheikh Ibn Uthaimin Allah ya masa yahama yana cewa:*
Ku kwadaitu wajen yawan karanta wuridin da suka samo asali daga al-Qur'an da kuma Sunnan Manzon Allah (saw), ga kuma irin wadan nan Wuridi: Kana karanta Ayatul Kursiyyu amma da niyya (tare da Samun Natsuwa akan cewa) zaka samu kariya daga Allah. 
Sabo da Manzon Allah (saw) ya ce:
*"Duk wanda ya karantata a cikin dare, ba zai gushe ba yana nan a cikin kariyan Allah, kuma Shaitan ba zai iya kusantarsa ba, har gari ya waye"*

*▪️قال الشيخ ابن عثيمين رحمه الله :*
احرصوا على قراءة الأوراد القرآنية والنبوية، ومنها: قراءة آية الكُرسي معتقدًا أن الله يحفظ بها ،

 • فقد قال النبي ﷺ : *(إِنّ مَن قرأها في ليلة لم يَزل عليه من الله حافظ ولا يَقْربه الشيطان حتى يُصبح)*

Idan kuwa mutane suka rafkana (wato basu damu da karanta ) irin wadan nan Wuridi ba, tanan ne Aljanu suke damunsu kuma kaga matsalar Aljanu tayi yawa.

• ولمّا غَفل الناس عن الأَوراد الشرعية كثرت فيهم الجِنّ وتلاعبت بهم . 📜لقاء الباب المفتوح

*Sheikh Ibn Bazz Allah ya masa rahama yake cewa:*

Duk wanda ya karanta wan nan aya a bayan ko wace Sallah, zata zame masa kariya daga ko wani irin Sharri, haka kuma karantata wajen yin barci, kamar yadda ya zo a Sunnah ta Manzon Allah (saw).


*▪️وقال الشيخ ابن باز رحمه الله :*
إذا قرأ المرء هذه الآية *[آية الكرسي]* خلف كُلّ صلاة كانت له حرزًا من كلِّ شرٍّ، وهكذا قراءتها عند النوم .. ،
فليقرأها عند النُّوم وليطمئن قلبه 📜مجموع الفتاوى

Akan haka muna jan hankali da mu dage muna karantar da yarammu muna kuma taimaka masu har muga suna karanta wadan nan wuridi , musamman ma tun daga yarinta.

⭕ حثوا أولادكم وساعدوهم على حفظها وبينوا لهم ثمرتها ؛ حتى يعتادوها صغاراً .

Allah ya kara bamu tsaro daga gareshi. 

✍️ Haruna Isah Muh'd
hdindima@gmail.com
*_______________________________*

No comments:

Post a Comment