Thursday, 17 March 2022

WANKAN JANABA

*⌛ AL-MAR'A ASSALIHA (ZAUREN MACE TA GARI)⌛*

*HADITH CLASS (5)*

*BABIN YADDA AKE WANKAN JANABAH*

✍️ *Haruna Isah Muh'd*
hdindima@gmail.com

*Hadith (1)*

١. *عن بن عباس قال حدثتني خالتي ميمونة قالت: أدنيت لرسول الله صلى الله عليه وسلم غسله من الجنابة فغسل كفيه مرتين أو ثلاثة ثم أدخل يده في الإناء ثم أفرغ به على فرجه وغسله بشماله، ثم ضرب بشماله الأرض فدلكه دلكا شديدا ثم توضأ وضوءه للصلاة، ثم أفرغ على رأسه ثلاث حفنات ملء كفيه ثم غسل سائر جسده ثم تنحى عن مقامه ذلك فغسل رجليه"*
رواه مسلم
An samu hadisi daga Ibn Abbas (Abdullahi dan Abbas) ya ce: Ummata Maimunatu (Matar Manzon Allah (saw)) ta bani labari, ta ce:
*" Na kusanci Manzon Allah (saw) lokacin da yake wankan Janaba, sai ya wanke tafukan hannayensa sau biyu ko sau uku, sannan ya shigar da hannayensan cikin abun wankan, san nan ya kwaranya ruwa a farjinsa(al'auransa) ya kuma wanke (al'auransan) da hanun haguna, san nan ya buga hanun a kasa ya cuccudesu sosai , san nan sai ya yi alola irin alolansa na Sallah, San nan sai ya kwaranya ruwa a kansa da kamfata uku kuma cikin tafin hanunsa, san nan sai ya wanke Sauran jikinsa (ya fara da tsagin dama kafin na haguna), san nan sai ya dan matsa daga inda yayi wankan (kadan) , san nan sai ya wanke Kafafunsa"*

Wan nan shi ne mafi cikan yadda ake wankan Janaba ko na Al-ada ko na Eed na karamar Sallah ko na Babban Sallah.

Allah yasa mu dace.

*___________________________*

No comments:

Post a Comment