*⌛ AL-MAR'A ASSALIHA (ZAUREN MACE TA GARI)⌛*
*HADITH CLASS (6)*
*BABIN YADDA AKE WANKAN JANABAH*
✍️ *Haruna Isah Muh'd*
hdindima@gmail.com
*Hadith (2)*
*_عن أم سلمة قالت قلت يا رسول الله إني امرأة أشد ضفر رأسي أفأنقضه لغسل الجنابة؟ قال لا، أنما يكفيك أن تحثي على رأسك ثلاث حثيات ثم تفيضين عليك الماء فتطهرين_*
رواه مسلم
*(Hadith 2)*
*_"An karbo Hadith daga Ummu Salma (RA) ta ce: na ce wa Manzon Allah (saw) ni mace ce mai yawan kisto a kaina, yanzu sai na warware in zan yi wankan Janaba?! Sai ya ce mata a'a, kawai ya wadaceki ki dinga yayyafa ruwa akan har sau uku (wato kina saka hanu kina jikashi kina shafe kayin har sai kinji ruwa ya taba kasan gashin) san nan sai ki kwaranya ruwa a jikinki, har ki tsarkaka"_*
NB
Hakan yana gwada mace mai kitso ko yawan gashi ba sai ta warware ba a wajen wanka, tana dan zuba ruwa a hankali har sai ta ji kasan gashin ya samu ruwa. Amma fa banda wankan Al'ada ko kuma wacce ta sanya mai a gashinta wanda duk yadda aka yi ruwa ba zai shiga ba, su kam dole sai sun warware.
*_"عن عائشة قالت كنت أغتسل أنا والنبي صلى الله عليه وسلم من إناء واحد من جنابة"_*
*(Hadith 3)*
*_"An samo Hadith daga Nana Aishatu (Ra) ta ce: na kasance ina wanka ni da Manzon Allah (saw) a abun wanka daya kuma wankan Janaba"_*
NB
Wan nan na gwada yadda ya halatta mata da miji su yi wanka tare, kuma yana daga cikin gwada soyayya a tsakani. Kuma a kasa akwai bayanin cewa ba laifi ba ne dan MA'AURATA sun ga al'auran juna.
Allah ya karba mana Ibadunmu baki daya. Ameeeeen
*___________________________*
No comments:
Post a Comment